Ko Ka So, Ko Kada Ka So, Biafra Ta Kusa Kafuwa, Nmandi Kanu Ya Fadawa Buhari..
Shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya yi zargin cewa gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari za ta zabi kungiyar Boko Haram a kan sake fasalin da kuma kuri’ar raba gardama da wasu ‘yan Najeriya ke neman a yi.
Kanu, wanda kuma shi ne Daraktan Rediyon Biafra, yana neman Jamhuriyar Biafra ne.
Tun a lokacin gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta haramta kungiyar tasa, IPOB wacce ke neman ballewa daga Najeriya.
Kamar Kanu, kungiyar fafutukar tabbatar da ikon mallakar kasar Biyafara (MASSOB) ita ma tana fafatawa iri daya tare da sauran kungiyoyin da ke rajin kafa Biafra a Najeriya.
Duk da haka, Kanu ya shiga shafin yada labarai na yanar gizo, Twitter, inda ya ambaci fadar Shugaban Najeriya cewa: “Ba za mu mika wuya ga barazanar sake fasalin kasa ba.” A kan wannan bayanin, Kanu ya ce a yanzu babu shakka tsakanin tsakanin sake fasalin kasa, raba gardama da BokoHaram, “mummunan Gwamnatin Najeriya” za ta zabi kungiyar ta Boko Haram, wannan ya ce saboda wadanda ke kan shugabancin masu ba da shawara a Najeriya “duk ISLAMIC / Fulani ne. ” Shugaban IPOB din ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: “LABARI:“ Ba za mu mika wuya ga barazanar sake fasalin kasa ba ”- @NGRPresident “Yanzu babu shakka tsakanin sake fasalin tsarin mulki, raba gardama & BokoHaram, wannan mummunan Gwamnatin ta Najeriya zata zabi #BokoHaram, saboda kawai dukkansu sunada ISLAMIC / Fulani. Ko ka so ko kada ka so, # Bifra ta kusa.” In ji shi.