Ilimi

Ko Kasan Jsmi’o’i Da Polytechnics Da FCE’s Da Sauransu Suna Da Hurumin Amshe Result Dinka Kofa Bayan Ka Gama Da Shekaru Ko Nawa Ne?

Kuskure ne saka Result din ka a Social Media

Sanya sakamakon kammala karatu na Degree, Diploma, NCE da sauran su a Social Media wani abu ne da ya zama ruwan dare ga daliban mu na Nigeria, inda suke ganin wani burgewa ne a duk lokacin da ka kammala karatun ka, ka amshi result dinka, ka sanya shi a duniyar Social media inda kowa zai iya samun access dashi, to wannan ba karamin kuskure bane, kuma ba abun burgewa bane, duk da wasu sun sani wasu kuma basu sani ba, domin kuwa yanzu fa duniya taci gaba, yin hakan ka iya haifar maka da wasu matsalolin da baka tunane, Misali:
1-Wani Zai iya zuwa ya dauki hoton wannan result din naka yaje yayi Scanning ya rika amfani dashi amatsayin nashi ne. Wanda ni akan hakan ganau ne ba jiyau ba. Kaga kenan ya zama kura da shan bugu; gardi da amshe kudin.

2-Idan kuma amfani kawai yake yi dashi to kayi sa’a. Dan kuwa wani zai iya amfani da sakamakon naka ya aikata wani laifi kaga su hukuma Details dinka suka gani dan haka kai zasu nema, kuma ba kada wata mafitar cewa ba kai bane, koma kana da ita to kan a gane ka sha wuya.

3-Sannan Makarantar da kayi zata samu saukin amshe sakamakon da ta baka aduk lokacin da aka samu akasi watakila wani ya aikata ba daidai ba da result din naka koma kai karan kanka ka aikata ba daidai din ba. Domin kuwa jami’a tana da hurumin da zatayi invalidating result dinka a duk lokacin da ka aikata laifin da yakai ayi maka hakan.

Gashi dai mun gani ga wani dalibin Engineering a Jami’ar ABU dake Zaria da ya daura kayan shaye-shaye a result din nasa, kuma Jami’ar tasha alwashin yin invalidating result din.

4-Sannan akwai masu buga result na bogi wanda idan ka saka naka result din a Social Media to zasu iya daukar sa su buga suyi gyare-gyaren su, suje su rika siyar maka da result akan kudi Naira 2000 kacal bayan ka shekara 3 ko 4, ko 5 ko 6 kana wahala. Haka wadanda aka kama suna siyar da na Jami’ar maiduguri suka bayyana.

Dan haka shawarar da zan bawa ‘yan uwa na dalibai shine: gaskiya idan ka taba saka wani result dinka a social media to ka goge, idan kuma baka saka ba, ko baka taba ba, to kar ka saka, illa iyaka ka rubuta “Ni wane na kammala Diploma na ko Degree na a makaranta kaza na samu sakamako kaza dan haka ku tayamu da addu’a” shikenan ya wadatar. Idan kuma kana ji cewa kai fa dole saika saka hoton result din naka a Social Media dan asan cewa ka gama, to ka tabbata ka rufe Serial Number na jikin result din naka, to koda wani ya samu Copyn yayi wani abu dashi to Insha’Allah ba zata shafe ka ba.

Sannan ka tabbata ka rufe Registration Number dinka. Saboda da wannan Serial Number din Makarantar ku zata iya tracing Profile dinka dan daukar mataki a kanka, bare kuma Registration Number, amma idan ka rufe su to kaga shikenan sai ka saka abunka lafiya lau ne.

Shima dalibin na Jami’ar ABU ta hanyar Serial Number din sa ne Jami’ar ta gano shi, Saboda ya rufe suna, regiatration Number, amma ya manta bai rufe serial Number ba, kamar yadda kuke gani a hoto.

Dan haka sai mu kiyaye, Allah ya kiyaye mu.
Allah ya kyauta, Amin.
Bissalam
Shehu Rahinat Na’Allah
9th July, 2020

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button