Ko kasan waye Abiyola ?
Cif Moshood Kashimawo Olawale Abiola shi ne cikakken sunansa.
Tun kafin zaben 1993, sunan Cif Abiola ya karaɗe lungu da sakon Najeriya, musamman yankin kudu maso yammacin ƙasar saboda shaharar da ya yi a fannin kasuwanci da taimakon marasa galihu da wallafa jarida.
An haifi M.K.O. Abiola a birnin Abeokuta na jihar Ogun a 1937
Kafin haihuwarsa, mahaifinsa ya haifi ‘ya’ya 22 amma dukkansu sun mutu suna jarirai. Don haka shi ne ɗansa na farko da bai mutu ba.
Tun yana ƙarami ya nuna ƙwarewarsa a fannin kasuwanci, kuma yana ɗan shekara tara ya soma sayar da itace.
Yakan tashi da duku-duku ya shiga daji inda yake saro itace sannan ya ɗora shi a amalanke ya shiga da shi gari domin sayarwa kafin ya yi shirin tafiya makaranta.
Ya kammala makarantar sakandare ta Baptist Boys High School Abeokuta, inda ya yi fice saboda ƙwazonsa.
Hasalima, Abiola ne ya zama editan jaridar makarantar mai suna The Trumpeter.
A shekarar 1956 Moshood Abiola ya soma aiki a matsayi kilak a bankin Barclays da ke Ibadan,
Bayan shekara biyu ne ya koma hukumar hada-hadar kudi ta yankin yammacin Najeriya a matsayin babban Akawu, inda daga bisani ya tafi birnin Glasgow na Scotland domin ci gaba da karatunsa.
MKO Abiola ya kammala Digirinsa na farko a fannin Akawu.
Lokacin da ya koma Najeriya, ya yi aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Lagos da kamfanin hada magunguna na Pfizer da kuma kamfanin ITT Corporation inda ya zama mataimakin shugaban kamfanin na Amurka da ke kula da Afirka da Gabas ta Tsakiya.
A can ne ma ya samu yawancin arzikinsa.
Hakan ne ya sa ya kafa gidan jaridar Concord da gidan gona na Abiola Farms da kamfanin buga littattafai da gidan biredi da kamfanin jirgin sama da kamfanin man fetur da bankin Habib da kulob ɗin kwallo kafa da dai sauransu.
Cif MKO Abiola ya shiga harkokin siyasa tun yana matashi inda ya shiga jam’iyyar National Council of Nigeria and the Cameroon (NCNC).
Kazalika ya shiga jam’iyyar NPN a shekarar 1980 kuma an zabe shi a matsayin shugaban jam’iyyar na jiha.
Sai dai bai yi fice a fagen siyasar ƙasar ba sai a lokacin da gwamnatin mulkin soja karkashin jagorancin Janar Ibrahim Babangida ta soma shirin mika mulki ga farar-hula inda ya tsaya takara a jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) bayan ya kayar da Ambasada Babagana Kingibe da Alhaji Atiku Abubakar a zaben fitar da gwani gabanin zaben shugaban kasa da za a yi ranar 12 ga watan Yunin 1993.
Cif Abiola ya zabi Ambasa Kingibe a matsayin mataimakinsa inda suka fafata da Alhaji Bashir Othman Tofa na jam’iyyar National Republican Convention (NRC).
An ayyana zaben a matsayi wanda aka gudanar cikin gaskiya da adalci, inda Cif Abiola ya lashe shi a jihohi da dama da suka hada da arewacin kasar inda abokin hamayyarsa ya fito.
Sai dai shugaban mulkin soja Janar Babangida ya soke zaben kafin a kai ga ayyana wanda ya lashe shi.
Hakan ya jefa kasar cikin rikicin siyasa, lamarin da ya tilasta wa Janar Babangida sauka daga mulki bayan ya kafa gwamnatin hadin kan ƙasa karkashin jagorancin Cif Earnest Shonekan,
Daga bisani ne Janar Sani Abacha ya kwace mulki daga wurin Cif Shonekan.
A 1994 Moshood Abiola ya ayyana kansa a matsayin mutumin da ya lashe zaben 1993.
Daga nan ne kuma gwamnatin mulkin soja ta ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa-a-jallo bisa aikata laifin cin amanar ƙasa.
A shekarar ne aka kama Cif Abiola aka kulle shi a gidan yari.
An kashe matarsa ta biyu Alhaja Kudirat Abiola a birnin Lagos a shekarar 1996 bayan ta fito fili ta bayyana goyon bayanta ga mijinta.
Ya mutu a hannun gwamnatin sojin Najeriya a ranar bakwai ga watan Yunin 1998 a wani yanayi mai ɗaure kai.
Ya bar mata da ‘ya’ya da dama.
Daga Umar Gaya