Kimiya Da Fasaha

Ko kun san dalilin da yasa jirgin Titanic ya nutse a kasan teku? Lallai ba’a yiwa Allah izgili a zauna lafiya.

Spread the love

Titanic babban jirgi ne wanda Thomas Andrew wani dan kasar Ireland ya kirkira a shekarar 1909-1912 da karafuna sama da miliyan biyu. Jirgin na Titanic yana daukan akalla mutane dubu (3,320) a inda yake dauke da kananan jirage na jiran kota kwana har guda ashirin (20) a cikinsa.

A cikin dalilin nutsewar jirgin akwai yin amfani da karafuna marasa inganci wajen hada jirgin saboda bincike ya nuna cewa akwai sidaran Oxygen, Phosphorus, Sulphur da Manganese sosai a jikin karafunan da akayi amfani dasu wajen hada jirgin na Titanic.

Note: A Chemistry Wadannan sinadaran suna ragewa karfe karfi matuka ta yanda zai iya ballewa/karyewa cikin sauki”

Lokacin da aka kammala hada jirgin TITANIC wani dan jarida ya tambayi Thomas Andrew cewa “Yaya yanayin lafiyar Titanic din? Sai Andrew yace ai ko Allah da kansa [Astagfirillah}< bazai iya nutsar da jirgin Titanic a karkashin ruwa ba ballantana igiyar ruwa da sauran matsaloli/halittun cikin ruwa” 😭.

A ranar 15-April-1912 jirgin na Titanic a hanyarsa ta zuwa birnin New York na America daga Southampton (United Kingdom) ya daki kankara wanda hakan yayi sanadiyyar ballewar wani bangaren na jirgin tare da bawa ruwa damar shiga cikin jirgin wanda hakanne yayi sanadiyyar nutsewar jirgin a karkashin ruwa.

Allah baya son mutum mai Alfahari da fariya, lallai Allah shine sarkin sarakuna mai IKO akan komai da kowa.

Usman Umar Dagona.

  1. Winner of National Chemistry Competition.
  2. Golden Boy of 2023 African Scientists Forum.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button