Rahotanni

Ko kun San dalilin Rigimar Gwamna El_rufa’i da Gwamna Ganduje?

Spread the love

DALILIN DAYASA EL RUFA’I DA GANDUJE SUKE ZAMAN DOYA DA MANJA…

Masu karatu suna mamaki tare da neman Dalilin dayasa alakar Gwamna Ganduje na kano da Gwamna El RUFA’I na kaduna tayi tsami haka kuma ake zaman doya da manja nazari da hasashen mu ya tabbatar mana dacewa an fara zaman doya da manjan ne tun bayan lokacin da Gwamna ganduje ya tsige Sarki Muhammadu Sanusi Na II kan karagar mulkin masarautar ta kano kasancewar sarkin amini ne ga Gwamna El rufa’i tun na yarinta
bayan an tsige sarkin malam nasiru El rufa’i ya shiga matukar damuwa hakan yasa Gwamna yabi sarkin harzuwa garin awae dake Jihar Nasarawa inda Gwamnatin kano ta kai sarkin amatsayin wajen da zaiyi rayuwarsa ta gaba kowa dai yasan yadda Gwamna El rufa’i ya tsaya tsayin daka harsaida ya Tabbatar sarkin ya isa jihar lagos…

An jiyo Gwamna El rufa’i yana ta gwabama Gwamna Ganduje magana kala kala a kwana kwanan nan El’rufa’i yace yawancin masu dauke da corona a jiharsa almajirai ne kuma daga jihar kano aka kawosu har’ila yau Gwamna yace a bikin sallar da za’ayi na gobe da kansa zaije iyakar tsakin kano da kaduna ya tsaya harzuwa dare don ganin babu wani daga jihar kano daya shigo jiharsa ta kadunan..

masu hasashen na ganin faruwar hakan bashi rasa nasaba da tsige sarki Sanusi da Gwamna ganduje yayi a watannin baya…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button