Ko kun san mutumin da ya fi kowa arziƙi a Duniya baƙar fata ne?
Baƙaƙen fatar da suka kafa tarihi a Duniya
1- Mutumin da ya fi kowa arziƙi a tarihin duniya baƙar fata ne shi ne Alhaji Musa Keita Mansa (Mali).
2- Shugaban ƙasar da ya fi ƙima da shahara a idanun duniya baƙar fata ne shi ne Nelson Mandela (South Afrika ).
3- Babban ɗan gudun gasar tsere na duniya baƙar fata ne shi ne Usain Bolt (Jamaica).
4- Shugaban ƙasar da ya fi kowanne shugaban ƙasa ilmi a duniya baƙar fata ne shine Robert Mugabe na ƙasar Zimbabwe (yana da masters a economist sannan da degree 8 a sauran fannoni).
5- ƴan wasan ƙafar da suka kafa tarihi a ƙwallon ƙafa ɓaƙaƙen fata ne wato Pele da Ronaldinho (Brazil).
6- Babban ɗan damben da ya fi kowa ƙarfi a duniya baƙar fata ne shi ne Muhammad Ali (Amurka).
7- Ɗan wasan golf wanda yafi shahara da arziƙi baƙar fata ne shine Tiger Wood.
8- Ƴar wasan Tennis wacce tafi shahara ɓaƙar fata ce ita ce Serena William.
9- Mawaƙin Pop wanda yafi kowa shahara A duniya baƙar fata ne wato Michael Jackson.
10- Babban mawaƙin Hip Hop baƙar fata ne wato 2Pac.
11- Manyan Philosophers na duniya baƙaƙen fata ne wato Malcon X da kuma Martin Luther.
12- Sai dai shugaban ƙasar da ya fi kowanne shugaba ƙarancin ilmi shima ɓaqar fata ne wato Jacob Zuma na South Africa .
Daga Mutawakkil Gambo Doko.