Labarai

Ko Kun zabe ni ko Baku zabe ni ba dole nine Shugabanku ba zan nuna banbanci ba ~Shugaba Tinubu.

Spread the love

Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a hada kai domin daidaita kasar, yayin da ya tunatar da ‘yan Najeriya cewa shi ne jagoransu ba tare da la’akari da jam’iyyar da suka zaba a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu ba.

Dole ne mu inganta haɗin kai da kwanciyar hankali ga kowa. Ko kun zabe ni a lokacin zabe, ko Baku zabeni ba ni ne Shugaban ku. Zan yi aiki a madadinku don ganin an samu sauyi na wadata,’’ in ji Mista Tinubu.

Shugaban, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dele Alake, ya fitar a ranar Asabar din da ta gabata, ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da ‘yan Najeriya mazauna kasar Faransa, inda ya halarci taron kwanaki biyu na tattalin arziki da gwamnatin Faransa ta shirya.

Da yake bayyana yadda ya cire tallafin man fetur nan take, Mista Tinubu ya ce “muna da kalubalen sufuri, kalubalen wutar lantarki, kalubalen ababen more rayuwa da sauransu.

Mista Tinubu ya hau kan karagar mulki ne a ranar 29 ga watan Mayu, bayan ya lashen zaben Mai cike da kabilanci da addini a kasar.

Matakin da ya dauka na yin takara da wani dan uwansa Musulmi, Kashim Shettima, a matsayin mataimakin shugaban kasa, ya jawo kakkausar suka daga al’ummar Kirista da suka yi ikirarin cewa Mista Tinubu na da Shirin Musuluntar da Nageriya.

‘Yan Najeriya da dama, musamman ma matasa, wadanda suka raina tsawon shekarun da aka yi a siyasance, sun goyi bayan tsohon gwamnan Anambra Peter Obi na jam’iyyar Labour a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu. Har yanzu dai suna ganin an tabka magudi a zaben da aka yi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button