Ko kunsan Gasar 20,000 Yasa Bidiyon Matan Aure?
Ko kun san Aisha Falke malamar Mata itace ta Saka Gasar N20,000 domin wakar Jaruma ga matan aure
Malama Aisha falke itace wacce take shirin mai Suna IZUWA GA FALKE a gidan television din Arewa24 nasan masu karatu basu bukatar dogon bayani game da Bidiyon matan auren da akayi yayi a wannan sallah Sai dai Jama’a da dama sunsha Tambaya ko ina wannan Bidiyon ya samo asali?
Hakane kuna da gaskiya masu Tambaya kunsan Ance komai Bashi rasa dalilin faruwarsa…
Shirin Da Malama aisha Falke take gabatarwa a Arewa24 shirin ne daya shafi matsalolin zaman takewar aure shirine dake karbar korafe korafen mata haka zalika shiri ne dake bawa mata damar turo wasikunsu kala kala,Ita Falke acikin shirin tana basu shawarwari hakan yasa aisha falke take da tarin yawan mabiya mata a shafukanta na sada zumintar zamani Falke tana kiran masu bibiyarta da suna ‘YAN AJI
Ranar Sallah ne Kawai Aisha Falke Ta saka Gasar Rawa ga yan ajin nata rawar mai salon taku daya bayan daya izuwa gaban mijin aurensu haka zalika aisha harma ta saka gasar Naira dubu Ashirin N20,000 ga duk wacce ta cinye gasar ta rawa…
haka yasa mata suka dunga daukar Bidiyo tare da wakar mawaki hamisu Breaker suna turawa zuwa ajinsu na malama aisha falke…
To Kunji dai dalilin Fitowar Bidiyon matan tare da nuna soyayya ga mazajensu…