Siyasa

Ko kunsan irin salon da kwankwaso yabi ya ya kayarda su Ganduje a Edo

Spread the love

Tabbas Banyi mamakin Godiyar da Goodwin Obaseki ya mikawa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba Akan nasarar Da yayi a wannan zabe Da akayi sannan banyi mamaki ba Akan kalaman Da shima Kwankwason ya fada ba acikin sakonsa Na Taya murna ga Obaseki Inda yake cewa nasarar Obaseki nasarar Kwankwasiyya ce.

Wannan daki Da kuke Gani shine Situation Room Na Jam’iyyar PDP ma’ana wurin DA Jam’iyyar PDP zata dinga bibiyar yadda zaben Ke tafiya musamman sakamakon zaben Kuma an Samar Da Dakin ne bisa shawarar Kwankwaso Da ya bayar a Lokacin Da yaje Jihar Domin nemawa Obaseki kuri’un Yan Arewa mazauna can.

Bayan an kirkiri wannan daki Na Situation Room kwankwaso yayi lacca Mai dauke hikimomi da dabaru ga matasan Da zasuyi aiki a wannan daki Na Situation Room Kuma Alhamdulillahi an Samu dukkan wata nasara Da Ake nema Domin wannan daki ya taimaka korai Da gaske wajen dakile wasu Daga cikin Shirye shiryen APC Na tafka Magudi. Daga Khadija Garba Sunusi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button