KO KUNSAN MASARAUTAR HADEJIA ITA CE TA YAKI TURAWA?

Spread the love

Masarautar Hadejia ita ce masarautar da ta yaki turawan mulkin mallaka a cikin masarautun kasar Hausa yayin da turawan suka shigo Arewacin Nigeria suka gina gidaje a manyan masarautun a shekarar 1906 domin bin umarnin su.

Amma haka sarki Hadejia Muhammad yaki bin umarnin su, domin kare martabar da jaddada Addinin muslunci,haka yayi shahada ya yake su, kuma Allah ya bashi nasara a kan su, wanda har yanzu kabarin commander sojojin wanda ake kira da captain Phillips da gidajan suna nan a Hadejia.

Shiyasa ake kiran sa sarki Mai Shahada, sannan Sultan yake kiran sa da sarkin yakin sarkin Musulmai

A wakar Shata ta sarkin Hadja Maje yana cewa

“Tsaya lokacin da nasara tataso tazo Birnin Hadejia fada sun sha kashi cikin fadama, mai Mamaki bar Mamaki maza jeka a binciko a fadi”

Daga Umar Gaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *