Labarai
Koda Buhari Ya Sauka Daga Mulki Ba Lallaibane Matsalolin Najeriya Su Warware Ba, Inji Olu Falae.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Tsohon minista kuma dan takarar shugaban kasa a shekarar 1999, Olu Falae ya bayyana cewa koda shugaba Buhari ya sauka daga Mulki ba lallau matsalolin Najeriya su kwaranye ba.
Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da manema labarai na Independent inda yake mayar da martani kan cewar da PDP ta yi wai shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sauka daga Mulki.
Yace babbar matsalar itace koma wanene ya hau mulkin kasarnan dole ya bi kundin tsarin mulkin Najeriya. Mun fahimci Falae yace kuma caccaki gwamnatin shugaba Buhari inda yace yawanci mutanen Katsina ya baiwa mukami.