Labarai

Korana bata kashe mutun dari biyar ba a Kano..

Spread the love

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya karbi rahoton kwamitin binciken mace mace da akayi a Kano a watannin baya karkashin jagorancin Maaikatar Lafiya ta jiha tate da hadin gwiwar hukumar NCDC ta kasa, da kuma kungiyoyin lafiya na kasashen waje kamar su Kungiyar Lafiya ta Duniya wato World Health Organisation WHO, da ta UNICEF, da kungiyar DFID Lafiya, da E-Health, da kuma Afenet.

Binciken wanda aka gabatar da shi na tsahon wata biyu daga ranar 2 ga watan March zuwa ranar 2 ga watan May, ya tattera bayanai ta hanyar abunda ake kira verbal autopsy wato bincike ta hanyar tambaya, sannan daga binciken da aka yi an gano cewa kashi 15.9% daga cikin 100% na wadanda suka rasu a wannan wata biyun, ake zargin cutar Corona wato Covid-19 ce ta kashe su ko kuma ta taso da wasu cutuktukan da su kai sanadiyar rasuwar su.

Wannan rahoto ya kawo karshen rade radin da ake na cewa daruruwan mutane ne suka rasu sakamakon cutar Corona, wanda wannan bincike na masana kuma wanda duk wadannan kungiyoyin da su aka aiwatar da shi, ingantacce kuma gamsasshe, ya kara da cewa akwai wadanda rashin zuwa asibiti ne ya yi sanadiiyar rasuwar su, sannan kuma rashin samun kulawa a asibitoci saboda dokar hana zirga zirga shi ma ya janyo mace-macen.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Hon Aminu Tsanyawa ne ya mika rahoton ga Gwamna Ganduje, bayan Farfesa Gadanya ya yi fashin baki akan rahoton, wanda daga bisani wakilan kungiyoyin da aka hada rahoton da su suma su ka yi bayani akan ingancin rahoton.

Gwamna Ganduje na tare da mataimakin sa Dr Nasiru Yusuf Gawuna da Sakataren Gwamnati Alhaji Usman da shugabar maaikata ta jihar Kano Hajia Binta, da Kwamishinoni da sauran manyan jami’an maaikatar lafiya da na Gwamnati.

Salihu Tanko Yakasai
Special Adviser Media
Government House Kano
June 16, 2020.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button