Rahotanni
Korona ta halaka Wasu mutun biyu a Kano…
Cutar Sarkewar Numfashi Da Akafi Sani Da Korona Ta Sake Hallaka Mutane Biyu A Kano.
Daga Haidar H Hasheem Kano
Mun samu rahoton cewa, mahukuntan lafiya a jihar Kano sun sanar da karin mutane biyu da cutar korona ta hallaka a jihar.
A halin yanzu dai cutar korona ta yi sanadiyar ajalin mutane uku a jihar. Ma’aikatar lafiyar jihar ce ta sanar da hakan da misalin karfe 12.15 na ranar Litinin, 27 ga Afrilun 2020 a kan shafinta na Twitter.