Kotu ta bayarda umarnin a Kai Mahadi Shehu gabanta a maimakon rike shi a hannun ‘yan Sanda.
Babbar Kotun FCT da Hon. Mai shari’a H. Mu’Azu ya umarci Mohammed Adamu, Sufeto Janar na ‘yan sanda ya gabatar da Mista Mahdi Shehu a gaban Kotu ranar Laraba, 9 ga Disamba 2020.
Mai Shari’a Mu’azu ne ya ba da wannan umarnin a ranar 4 ga Disamba 2020 bayan ya saurari Lauyan Mista Mahdi – Mista Madu Joe-Kyari Gadzama na J-K Gadzama LLP, Abuja wanda ya yi jayayya a gaban Kotu game da wannan.
Idan dai za a iya tunawa, ‘yan sanda sun tsare Mista Mahdi Shehu a Abuja a ranar 25 ga Nuwamba 2020, kuma tun daga lokacin ya shiga hannun‘ yan sanda wanda a inda a ke tsare da shi wani katon maciji mai dafi ya ciji Mahadi a ranar 25 ga Nuwamba Nuwamba 2020.
Kotun ta kuma gayyaci IGP din don ya nuna dalilin da ya sa ba za a saki Malam Mahdi ba kuma an gabatar da bukatar neman hakkokinsu na musamman a ranar 9 ga Disamba, 2020.