Labarai

Kotu ta buƙaci mawaki Rarara ya gurfana a gabanta bisa zargin boye matar aure na Tsawon wata uku.

Spread the love

Wata kotun Shariah da ke Kofar kudu a Kano ta gayyaci shahararren mawakin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Dauda Kahutu Rarara da ya bayyana a gabanta a ranar 22 ga watan Disamba kan zargin alaka ba bisa ka’ida ba da kuma boye matar aure, mai suna (wanda aka sakaya) wanda ta fito a daya daga cikin bidiyon wakokinsa.

Wani korafi kai tsaye da mijin matar ya gabatar a gaban kotu ya yi ikirarin cewa mawakin ya yi amfani da matarsa, matar aure a cikin bidiyon wakar da ya yi kwanan nan mai taken ‘Jihata, Jihata ce’ bayan da har yanzu ba a san inda take ba.

Ya kuma yi zargin cewa tsawon watanni uku ba a san inda matar tasa take ba saboda Haka yana rokon kotu da ta shiga tsakani da yin adalci kan abin da aka yi masa.

Alkalin Kotun Shariah Ustaz Ibrahim Sarki Yola ya sanya ranar 22 ga Disamba don ci gaba da shari’ar kuma a ba da sammaci ga Rarara don ya bayyana a ranar da za a fara shari’ar

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button