Siyasa

Kotu Ta Dage Sauraren Karan Da Abba Gida-Gida Ya Shigar Kan Gwamna Ganduje.

Spread the love

Rahotanni daga jihar Kano sun bayyana cewa kotun jihar ta dage karar da dan takarar Gwamna na jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2019, Abba K Yusuf ya shigar da gwamnatin jihar inda yake kalubalantar sayar da wasu kadarorin jihar.

Lauyan Abba, Bashir Yusuf Tudun Wazirci ya bayyanawa kotun cewa sayar da kadarorin da gwamnatin jihar taje ya sabawa doka. Saidai wakilin Gwamnati kuma kwamishinan shari’a, Barista Musa Abdullahi Lawal ya bayyana cewa wannan ikirari bashi da tushe ballantana makama.

Mai shari’a Nura Sagir ya dage sauraren karar zuwa 29 ga watan Octoba, kamar yanda Freedomradio ta ruwaito.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button