Kotu ta tasa keyar Sowore zuwa Gidan Kaso.
A Yau litinin ne wata Kotun Majistare, dake zaune a Wuse Zone 2 a Birnin Tarayya ta Tasa Keyar Omoyele Sowore, zuwa gidan Gyaran Hali na Kuje.
Sowore dai shine shugaban gidan Jaridar Sahara Reforters, kuma Jami’an Tsaron Najeriya sun Kamashi ne a Abuja ranar Alhamis 31/12/2020, a lokacin da suka shirya zanga zanga bayan Gwamnatin Tarayya ta Haramta Irin tasu zanga zangar.
Kotun ta Zargi Sowore da Aikata laifuka Uku, da Suka hada da- Hada Taro ba bisa ka’ida ba, Yin Haramtacciyar Zanga Zanga da Tunzura Jama’a domin su tada yamutsi.
Sai dai wanda ake zargin ya Musanta zargin da Ake Masa.
Bayan Kamashi da Akayi ne Ake ta yada Hotunan Sa da Rauni a Fuskarsa, Inda masu Bashi kariya suke cewa Jami’an Tsaro suncin zarafinsa.
Shi dai Sowore, yayi takarar Kujerar Shugabancin Kasar Nan A Shekarar 2019, a Jam’iyyar AAC.
Ko a shekarar da ta gabata na 2020, Sowore, ya Tai maka wajen Ingiza Wutar Zanga Zangar #EndSars, wanda yayi Sanadiyyar Salwantar Rayuka da Dukiyoyi a Kasar Nan.
Sowore, Shi ya Jagoranci Zaman Dirshan na Ganin Anyi Juyin Mulki a Kasar Nan.
Ahmed T. Adam Bagas