Uncategorized

Kotu Ta Umurci EFCC Ta Biya Dauda Lawal Diyyar Naira Miliyan 20.

Spread the love

Wata babbar kotu dake zamanta a Legas, Karkashin Mai Shara’a Muslimu Hassan, Ta Umarci Hukumar Yaki da cin hanci da Rashwa ta Biya Tarar zunzurutun kudi har Miliyan 20, ga Dauda Lawal, Saboda EFCC ta Tsare shi har Kwanaki 13, Domin Hukumar ta Bukaci yabasu Cin hanci har na Dalar Amurika miliyan 2, Yace bazai bayar ba.

Tun shekaru biyar da suka gabata ne dai Hukumar EFCC, karkashin jagorancin Ibrahim Magu, Suka Kama Dauda Lawal, da wasu mutane Uku, domin ya Sanya Wasu kudi masu yawa a Asusun Ajiyarsa na Banki.

Bayan EFCC, ta kamasu ta Kulle Asusun Ajiyarsu, EFCC Bata gurfanar dasu gaban Kotu ba, sai ta Bukaci Kowa ya biya Dala miliyan 2 a Sake shi kuma abude masa asusun sa.

“Sai dai daga mutane Uku ba’a san ko ya akayi dasu ba, ko dai sun biya wannan tarar ko kuma basu biya ba.

“Shi Dauda Lawal, yace bazai bada Cin hanci ba har na dala miliyan 2, sai EFCC ta bukaci Yabada dala miliyan 1, Sai a barshi kuma a bude asusun sa, Idan ba haka ba Za’a Turashi Kotu.

EFCC sun Kulleshi har tsawon kwanaki 13, ba tareda sun Gurfanar dashi Kotu ba.

Lawal din yayi wannan Jawabin ne, makon da ya gabata a Gaban Ibrahim Magu, a Gaban Kwamitin nan da Shugaba Buhari ya kafa domin gudanar da bincike kan Zarge- Zargen da Akewa Magu, Kwamitin karkashin Jagorancin Mai shara’a Ayo Salami.

Sai dai daman Ire Iren wadannan Abubuwan da ake zargin Magu shine ya sanya Shugaban kasa Buhari, ya Sallami Magu daga Hukumar EFCC, kuma ake Tsare dashi ya Amsa Tambayoyi.

Bayan Kalaman da Dauda Lawal din yayi a gaban Kwamitin, Magu yana Wajen kuma bai Yi Musu ba.

Daga Karshe dai yanzu Kwamitin Ayo Salami, tace zata bibiyi kadarorin da Magu yace ya karbo hannun Barayin Gwamnati domin ta Tabbatar da Adadinsu da kuma Inda suke, Kafin a Mikasu ga Gwamnati.

Ku kasance Da mu domin jin Ina Aka Kwana kan Wannan Lamari….

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button