Kotu Ta Wanke Shekarau Game Da Watandar Kudin Kamfen Din Jonathan N950m Wanda Aka Raba A Gidansa.
Kotun daukaka kara, reshen Kano, ta sallami tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, bisa zargin hadin baki da karbar zunzurutun kudi Naira miliyan 25 ba tare da wucewa ta wata cibiyar hada-hadar kudi ba da kuma daukar nauyin kula da Naira miliyan 950.
Kudin, ana zargin an karbo su ba bisa ka’ida ba daga tsohuwar Ministan Albarkatun Man Fetur, Diezani Allson Maduekwe kuma aka raba tsakanin mambobin jam’iyyar Democratic Party (PDP) a Kano.
Da take yanke hukunci a jiya, Mai shari’a Amina Wambai, wacce ta gabatar da karar mai shari’a Abubakar Datti Yahaya, ta ci gaba da cewa EFCC ba ta sauke nauyin da ke kan Malam Shekarau ba, wanda ya kasance a ranar 27 ga Satumba, 2019 a Babbar Kotun Tarayya da ke Kano.
Mai Shari’a Lewis Allagoa, ya umarce shi da ya shigar da kara bayan da ba a shigar da karar da lauyansa ya gabatar ba.
Kotun daukaka kara ta tabbatar da cewa EFCC ta gaza kafa alakar da ke tsakanin Mallam Shekarau da kuma kudin da suka kai Naira miliyan 25.
Kotun ta kuma ce hujjojin da dukkanin lauyoyin suka gabatar sun wanke Shekarau a cikin hadin baki na aikata laifi tsakanin Bashir Ahmad da Malam Ibrahim Shekarau kamar yadda EFCC ta yi zargi.
Hakazalika Kotun daukaka kara ta tabbatar da cewa EFCC ta gaza wajen tabbatar da cewa Mallam Ibrahim Shekarau ya shiga cikin rabon Naira miliyan 950 a gidansa, tana mai jaddada cewa masu gabatar da kara a gaban karamar kotun sun nuna cewa an tara N950 miliyan da aka karba daga Diezani Alison Maduekwe ba bisa ka’ida ba.
Ta ce kotun wurin adalci ne ba wai hasashe da jin magana ba.
Kotun ta ce babu wata hujja da za ta iya bai wa Mallam Shekarau damar buda kariya a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kano.