Mata iyayenmu

Kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 22 a gidan Yari, bayan ya yiwa ƴar kanwarsa Fyade.

Spread the love

Wata Babbar Kotun da ke zamanta a Calabar, babban birnin jihar Kuros Riba, ta yanke wa wani mai suna Emmanuel Thompson Udo, hukuncin ɗaurin shekara 22 a gidan yari, saboda yi wa ƴar kanwar shi mai shekaru 14 fyade.

An same shi da laifin yi wa Yariyar fyade ne a ranar 15 ga watan Agusta, 2018 a gidansa da ke kan titin No 54 Afokang, karamar hukumar Calabar ta Kudu.

Da take yanke hukunci a Yau Talata, Mai Shari’a E. E. Ita, Muƙaddashiyyar Babban Alkalin Jihar, ta yanke wa Udo hukuncin ɗaurin shekaru 22 ba tare da zabin biyan tara ba.

Amintaccen hukuncin nasa ya samu karbuwa daga kungiyar Basic Rights Counsel Initiative (BRCI); Hon. Tanko Ashang, Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Kuros Riba; Mista Felix Itittim, jam’iyyar DPP; Blessing Egwu da kuma Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya.

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button