Labarai

Kotu ta yankewa Bappa Alti hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda ya kashe ɗansa don yin tsafi dashi a Adamawa.

Spread the love

Wata babbar kotu a jihar Adamawa ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa saboda kashe dansa.

Mutumin, Bappa Alti na kauyen Ganji a karamar hukumar Gombi, zai mutu ta hanyar ratayewa saboda fille kan dansa, Buba Bappa, don yin tsafi dashi.

Babbar Kotun ta VII da ke Yola babban birnin jihar, wacce mai shari’a Fatima Tafida ke jagoranta, ta yanke wa Bappa, makiyayi hukunci, sbod laifin kashe dansa ta hanyar bugun shi da sandar kiwon shanu sannan kuma ya yanke kansa da adda.

An bayyana a ranar Alhamis cewa wasu matsafa sun nemi mai laifin da ya kashe dan nasa domin su samu kudi da kansa, sai kuwa ya fara shirin kisan.

An bayyana cewa mai laifin ya yi amfani da wata dama ce a ranar 13 ga Yuni, 2013 lokacin da shi da dan nasa suka je daji domin kiwon shanu.

Bappa an ce ya bugi ɗan nasa, sakamakon haka ɗan ya faɗi a ƙasa, sannan kuma ya yi amfani da adda da ke jikinsa don kammala aikin.

Lokacin da mai laifin ya dawo gida da yammacin ranar, sai ya nuna kamar bai san inda dan nasa yake ba, wanda hakan yasa masu neman yaron bulayi.

Kungiyar binciken wacce ta gano gawar dan ba a kai rana ta biyu ta bincike ba, ta fara zargin mahaifin kuma ta kama shi.

Hedikwatar rundunar yan sanda na yanki Gombi, wanda ya dauki lamarin, ya fara bincike, wanda sashen binciken manyan laifuka na Yola ya karbe shi inda Bappa ya amsa aikata laifin.

Daga baya an gurfanar da shi a gaban kotu saboda aikata laifin kisan kai wanda ta yanke masa hukuncin kisa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button