Labarai

Kotu Ta Yankewa Mawakin Da Yayi Wakar Batanci Ga Annabi(SAW)Hukuncin Rataya A Kano

Spread the love

Daga Yaseer Alhassan Gombe

Kotun koli ta Kano ta yankewa wani matashi mai shekaru 22 hukuncin kisa ta hanyar ratayewa saboda zagin Annabi Muhammad (SAW).

Kotun da ke zamanta a Filin Hockey ta Hausawa, wacce Khadi Aliyu Muhammad Kani ke jagoranta ta bayar da wannan hukunci ne a ranar Litinin bayan da ta samu Yahaya Aminu Sharif da laifi kamar yadda ake tuhumarsa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Sharif Aminu ya shirya waka ne a cikin watan Maris 2020, wanda a ciki yayi batanci ga Manzon Allah Muhammad (S.A.W).

Wakar da aka sanya a kafafen sada zumunta ta hanyar bidiyo ta haifar da rikici wanda hakan ya haifar da mamaye gidan mawakin wanda wasu matasa suka yi ƙokarin kuna shi.

An ce matashi mawakin yana cikin kungiyar darikar Tijjaniya kuma memba ne a kungiyar Faidha, “wanda aka san su da fifikon Shaikh Ibrahim Nyass kan Annabi Muhammad (SAW).”
Amma a wani martani, kungiyar Jam’iyayyatu Ansariddeen Attijaniyya ta nesanta kanta daga mawakin da ke zaune a Kano, ta kuma dauke wakar a matsayin sabo.

Sakataren kungiyar na kasa, Sayyidi Muhammad AlQasim Yahaya, a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ya ce sabanin rahotanni, Dariqatul Tijjaniyya da Sheikh Ibrahim Nyass suna da matukar kauna ga Annabi Muhammad.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button