Labarai
kotu tace Dole’yan sanda su biya ‘yan Shi’a milyan 15
Yau Litinin wata Babbar kotun Nageriya dake abuja ta umarci Hukumar yan sandan Nageriya da biyan ‘yan shi’a biya diyyar naira milyan sha biyar N15 million bisa kisan ‘yan shi’a ba tare aikata laifin komai ba
Hukumar yan sandan dai sun harbi mutun uku ne cikin mabiya mazahabar shi’a a lokacin da suke kan gabatar da zanga zangar luma kan a saki shugabansu Malam Ibrahim Zakzaky wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar su har lahira wa’yanda suka mutu a Lokacin sun hada da..
Suleiman Shehu, Mahdi Musa, Bilyaminu Abubakar Faska da kuma Askari Hassan a Ranar July 22, 2019…