Addini
Kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin kisan da aka yankewa matashin da yayi kalaman ɓatanci ga Annabi a Kano.
Kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin kisan da aka yankewa matashin da yayi kalaman ɓatanci ga Annabi a Kano.
Sashin ɗaukaka ƙara na Babbar Kotun Jihar Kano ta jingine hukuncin kisan da aka yanke wa mawakin Kano, Aminu Yahaya Sharif, saboda yin sabo.
Kotun ta ba da umarnin a sake sauraron shari’ar da ake yi wa Sharif wanda ya shigar da kara domin kalubalantar hukuncin.
Babban alkalin jihar, Nuraddeen Sagir ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis bisa hujjar cewa karar karamar kotun na cike da kura-kurai.
Sagir ya kuma ba da umarnin cewa a bai wa Sharif cikakkiyar wakilcinsa na shari’a kuma a yi shari’ar a gaban alkalai daban-daban.
Kamar yadda Jaridar Punch ta rawaito.