Labarai

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta kori kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi.

Spread the love

Wani kwamiti mai mutane uku a ranar Juma’a ya ce gudanar da zaben da ya samar da Suleiman a mazabar Ningi ta tsakiya a karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi cike da kura-kurai.

Kotun daukaka kara ta bayar da umarnin sake zabe a rumfunan zabe 10 da ke mazabar.

A halin da ake ciki kuma, shugaban masu shari’a a kan lamarin ya gargadi hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC da ta gudanar da al’amuranta kamar yadda doka ta tanada domin kaucewa jefa kasar nan cikin mawuyacin hali.

Da yake yanke hukunci a karar da aka shigar a mazabar Ningi ta tsakiya, ya ce INEC ta gudanar da zabukan 2023 ba a matsayin alkali mara son Kai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button