Labarai

Kotun daukaka Kara dake ta soke zaben Shugaban Majalisar jihar Kaduna.

Spread the love

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke zaben kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Liman, tare da ba da umarnin sake zabe a rumfunan zabe biyar.

Wani kwamitin alkalai uku karkashin jagorancin mai shari’a O. O. Adejumo ya yi watsi da karar da shugaban majalisar ya shigar tare da bayar da umarnin sake gudanar da zabe a rumfunan zabe biyar maimakon 42 da kotun ta bayar.

A ranar 30 ga watan Satumba ne kotun sauraren kararrakin zabe ta majalisar dokokin jihar Kaduna ta soke nasarar da Liman wanda ke wakiltar mazabar Makera ya samu tare da ba da umarnin sake zabe a rumfunan zabe 42.

Hakan ya biyo bayan karar da dan takarar jam’iyyar PDP, Solomon Katuka, ya shigar gaban kotun yana kalubalantar zaben Liman na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

A cikin karar da ya shigar, dan takarar na PDP ya yi zargin cewa an tabka kura-kurai game da zaben shugaban majalisar, inda ya ce a gaskiya shi ne ya lashe zaben majalisar da aka gudanar a mazabar Makera a ranar 18 ga Maris, don haka ya kamata a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

A hukuncin kotun daukaka kara, APC na da kuri’u 17,470 yayin da PDP ta samu kuri’u 17,088.

Kotun ta ce an soke zaben Liman ne bisa ka’ida ta farko, inda tazarar 382 tsakanin jam’iyyun biyu bai kai adadin PVC da aka tara a rumfunan zaben da abin ya shafa ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button