Nishadi

Koyarwa Da Ke Cikin Shirin Kwana Casa’in Ga Duk Wata ‘Ya Mace..

Spread the love

Kwana Casa’in, wato 90 Days a turance, shiri ne mai dogon zango da tshar Talabijin ta Arewa24 ke haskawa wanda a ranar Lahadi da ta gabata aka fara haska zangon farko na kashi na Uku (Season 3).

Ga duk mai kallon shirin ya san abin da ya faru da Fa’iza Lahab, tsohuwar budurwar Malam Ali. Ina so abin da ya faru da Fa’iza ya zamo ishara ga ‘ya’ya mata. ABIN DA YA FARU A TAKAICE: Fa’iza dai budurwa ce ga Malam Ali wanda ya kasance malaminta a jami’a. Ta na matukar son sa wanda hakan ya bata damar mallaka masa kanta ba bisa ka’ida ba. Ma’ana, ta bashi kanta ya san sirrinta na ‘ya mace har ya kai ga ta fita a kansa, daga baya kuma ya juya mata baya a lokacin da ta bijiro masa da batun aure. A ƙarshe ma Malam Ali ya koma soyayya da kanwarta har aka kai ga batun aure. Jan hankali: A duk lokacin da ‘ya mace ta lamunce wa namiji kanta har ya san sirrinta na ‘ya mace, to ta sani mafi yawa daga ciki a lokacin ne za ta ji ta bude wani sabon shafin so da kaunar sa amma kashhh. Shi kuma a wannan lokacin ne zai sa mata karan tsana a hankali a hanlaki zai janye mata. Kai, wani nan take ma zai nuna mata shi fa ya gama da ita. Ya ke ‘yar uwa mace, ki ji tausayin kanki. Ki guje amince wa duk wani da namiji da ya nemi ya sanki tun kafin aure. Ki sani, duk wanda zai iya bukatar haka daga gareki to hakika ba masoyinki bane na hakika. Kokari kawai yake yi ya san ni’imar ki ya tsallake zuwa gaba in auren ne sai dai ki ji labarin ya yi. Allah ya ƙara kare mana zuri’ar mu. Daga Isma’il Karatu Abdullahi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button