Tsaro

Ku Ba Mu Makamai Don Mu Yaki Ta’addanci A Kasarmu, Rokon Lai Mohammed Ga Shuwagabannin Duniya.

Spread the love

KU Ba Mu Makamai Don Mu Yaki Ta’addanci A Kasarmu, Rokon Lai Mohammed Ga Shuwagabannin Duniya.Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga kasashen duniya da kada su rika amfani da hujjojin da ba su dace ba da za su hana kasar nan mallakar manyan makaman da za su yaki ‘yan ta’adda.

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya yi wannan kiran a ranar Alhamis din da ta gabata yayin da ya gabatar da jawabi a dandalin Kamfanin Dillancin Labarai na NAN a Abuja.

“Ina son yin amfani da wannan damar in ce kasashen duniya na iya taimaka mana fiye da yadda suke yi a yanzu. “Domin yakar ‘yan ta’adda muna buƙatar makamai manya.

“Manyan kasashe duniya sun ki sayar mana da wasu muhimman makamai.” “Fiye da shekaru biyu zuwa uku yanzu mun biya wasu muhimman makaman da ba su fito da su ba har ma sun ki ba mu kayan aikin. “Roƙona a gare su shi ne, don Allah su taimaka wa Najeriya sa samar mana da waɗannan hanyoyin da za mu iya magance rashin tsaro da inganci”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button