Ku cigaba da hakuri da jajircewa ~IBB yayi Kira ga ‘yan Nageriya.
Tsohon Shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida (rtrd) ya roki ‘yan Najeriya da su kasance masu jajircewa, da kuma hakuri a yayin fuskantar dimbin kalubale da kasar ke fuskanta.
Babangida ya ba da wannan shawarar ne yayin wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Channels a jajibirin sabuwar shekara, ya kara da cewa duk abin da ya fara to tabbas yana da karshe.
IBB ta lura da cewa, cutar ta COVID-19 ta kasance babban kalubale ga duniya baki daya, har da Nijeriya, kuma ta shafi dukkan wasu fannoni na shugabanci.
Ya kuma roki ‘yan Najeriya da su yi biyayya ga ka’idojin COVID-19 kamar yadda wadanda ke kula da lafiya a kasar suka tsara.
“Ina yi wa dukkanmu fatan alheri kuma ina son mu kasance masu dorewa, mu kasance masu azama da haƙuri saboda duk abin da ke da farko [tabbas] yana da ƙarshe,” in ji tsohon Shugaban na Jiha.
“Ina ganin da zarar mun yi aiki tukuru don ganin an cimma manufofin daidai, za mu sami kyakkyawan yanayi mai kyau 2021
Don haka ina amfani da wannan damar inayi wa dukkanmu ‘yan Najeriya fatan alheri na 2021 kuma ina karfafa yan Najeriya da su ci gaba da taimaka wa gwamnati wajen magance duk matsalolin da ke tattare da shugabanci.
“2020 ta kasance wani lokaci mai matukar kalubale ba ga wannan kasar ita kadai ba harma Zuwa duniya. Covid-19, Kan yanayin tattalin arziki da kuma rashin tsaro.
“2020 ta kasance shekara mai kalubale ta fuskar lafiya, tsaro da tattalin arziki. Muna ci gaba da godiya ga Allah kuma za mu shawo kan wadannan matsalolin…. Coronavirus gaskiya ne. Don haka ina kira ga mutane su tafi tare da abin da masu kiwon lafiya suke ba mu,