Rahotanni
Ku cigaba da zama a Ondo, domin jihar ku ce, gwamnan Ekiti Kayode ya fadawa Fulani.
Shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya kuma Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi, ya bai wa Fulanin da ke zaune a jihar Ondo tabbacin cewa babu abin da zai sake samun su.
Inda ya ce su kwantar da hankalinsu, jihar Ondo gidansu ne, suna da ‘yancin Zama cikin Salama a Jihar.
Har wa yau ya yi gargadin a daina kabilantar da matsalar tsaron kasarnan, domin a cewarsa, matsalar ta shafi kowacce kabila a Nijeriya Inji Fayemi.