Ku Daina Tunzura ‘Yan Najeriya Da Maganganun Marasa Kyau -Gargadin Wata Kungiya Ga Obasanjo Da Soyinka.
Wata kungiyar farar hula Mai suna (CSO), Citizens Action for Good Governance (CAGG), a ranar Alhamis, a Abuja ta yi Allah wadai da kalaman da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya yi game da halin da kasa ke ciki cewa Najeriya ta zama kasar da ta gaza.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa sanarwar ta bata sunan gwamnatin da Muhammadu Buhari ke jagoranta a matsayin jagorantar kasar zuwa ga halaka.
Har ila yau, Farfesa Wole Soyinka, ya goyi bayan Obasanjo cewa kasar ta kusa zuwa ga halaka.
Idan za a iya tunawa, Obasanjo a ranar 13 ga Satumba ya yi ikirarin cewa Najeriya a karkashin Buhari ta zama kasar da ta gaza, yayin da Soyinka ya goyi bayan ikirarin nasa cewa kasar ta kusa karewa.
Da yake jawabi ga manema labarai a kan batun, Kodinatan CAGG na kasa Mista Nazir Galadanchi, ya ce fushin Obasanjo ya samo asali ne daga rashin iya jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, don ba a yin abin da yake so, da kuma kin amincewa da bukatar sa ta son kai.
“Kalamansa na baya-bayan nan da kuma ikirarin da yake yi na cewa Nijeriya a karkashin Buhari kasa ce ta gaza, abin takaici ne, maras hankali, karya ne kuma an yi shi ne a kan magana mara dalili.
Galadanchi ya ce “Abin mamakin shi ne, mutumin da ke da’awar shi ne Olusegun Obasanjo, wanda ake zarginsa da aikata ba daidai ba da kuma cin zarafin da ya yi yayin da yake kan mulki shine yafito yake wannan furucin.”
Ya zargin Obasanjo da girman kai da kuma kafa haramtacciyar doka ya hana biyan kudi ga gwamnatin jihar Legas saboda kawai banbancin siyasa zamanin Gwamna Bola Tinubu.
Galadanchi ya kuma yi zargin cewa Obasanjo ya yi wani yunkuri na ganin an gyara kundin tsarin mulkin 1999 domin ci gaba da mulkin kansa; a cikin hakan, ya koma ga dabarun “sasantawa” tare da juyawa ga ainihin wadanda ke ganin masu adawa da kudirin sa na rashin fahimta.
“Ya saki EFCC a kan abokan hamayyarsa kuma ya mayar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa zuwa karensa na kai hari kuma ya yi zargin ya tilasta wa Majalisun Dokokin Jiha a Filato, Bayelsa da Oyo don tsige gwamnoninsu ba bisa ka’ida ba.