Labarai

Ku fada Mana sunan Gwamnan dake daukar nauyin ta’addanci a Arewa ~Tanko Yakasai ga Apc

Spread the love

Wani dattijo dan arewa kuma mamba a kungiyar tuntuba ta Arewa, Alhaji Tanko Yakasai, ya bukaci All Progressive Congress da ta bayyana sunan gwamnan a yankin Arewa maso Yamma wanda suka ce shi ne ke haddasa karuwar ‘yan ta’adda da kashe-kashe, ta yadda’ yan Najeriya za su iya maganin sa.

Yakasai, shi ma dan kungiyar kafa cigaban Arewa, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da SaharaReporters a ranar Laraba, yana mai cewa APC, ba ta taimaka wa kasar nan ba idan Bata bayyana sunan Gwamnan ba
A ranar Alhamis din da ta gabata, jam’iyyar APC ta zargi wani gwamna daya daga cikin Gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma shida da cewa shi ke da alhakin yawaitar ta’addancin ’yan fashi da kashe-kashe a yankin.

Mista Yekini Nabena, mai rikon mukamin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC, ya ce “wani rahoton sirri” ya alakanta gwamnan da manyan kararraki na ‘yan fashi, satar mutane da sauran muggan laifuka a yankin.

Da yake magana da SaharaReporters, Tanko Yakasai ya ce ya kamata APC ta tona asirin gwamnan sannan ta bar ‘yan Najeriya su yi maganin sa.

Dattijon ya ce, “Su (APC) ba su gaya mana ko wane ne gwamna ba. Matsalar kenan. Ya yi kama da hasashe kawai. Don haka, ya kamata mu san ko wanene wancan gwamnan. Kowa na neman mafita kuma idan wani yayi ba daidai ba, to ya kamata su fallasa shi domin jama’a su nuna adawa da shi kuma ya daina.

“Idan suka rikewa kansu, to basa taimakawa kasar. Don haka, ina so su sanya sunan mutumin domin mu kawo karshen sa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button