Ku gaggauta Sako daliban da kuka Sace a kankara ~Majalisar Dunkin duniya.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da sace daliban Makarantar Kimiyya ta Gwamnati da ke Kankara, Jihar Kastina.
Kungiyar ta nuna damuwarta a cikin wata sanarwa da Kakakin Sakatare Janar Stéphane Dujarric, ya fitar a ranar Litinin.
Wasu ‘yan bindiga a kan babura sun afka wa makarantar Kimiyya ta Gwamnati da ke Kankara da yammacin ranar Juma’a. Sun shiga artabu da jami’an tsaro a cikin mummunan harin, wanda ya tilasta ɗaruruwan ɗalibai guduwa suka ɓuya a cikin daji da kewayen dajin.
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, wanda ya ziyarci makarantar a ranar Asabar, ya ce sojoji na aikin ganowa da kuma kubutar da wadanda aka yi garkuwar da su.
A ranar Lahadi, gwamnan ya lura cewa har yanzu ba a ga dalibai 333 ba.
Sanarwar ta ce, “Sakatare Janar ya yi tir da Allah wadai da harin 11 ga Disamba a kan makarantar sakandaren ta jihar Katsina, a Najeriya, da kuma rahoton sace daruruwan yara maza da ake zargin ‘yan fashi da makami ne.
“Sakatare Janar din ya yi kira da a gaggauta sakin yaran da aka sace ba tare da wani sharadi ba tare da dawo wa danginsu lami lafiya. Ya sake nanata cewa hare-hare a kan makarantu da sauran wuraren ilimi ya zama babban take hakkin dan adam. Ya bukaci hukumomin Najeriya su kawo masu alhakin wannan aikin zuwa ga adalci.
“Sakatare Janar din ya sake tabbatar da hadin kai da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ga gwamnati da mutanen Najeriya a yakin da suke yin ta’addanci, da mummunar tsattsauran ra’ayi, da aikata laifuka.”