Ku kasance masu adalci a ko da yaushe a cikin duk abin da kuke yi, Idan ka ga matsaloli suna faruwa ta ko’ina a kasa to akwai matsala game da adalci, sakon Sarkin Musulmai Ga Buhari da Gwamnoni.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, a ranar Talata a Abuja ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta Jiha da su tabbatar da adalci ga dukkan ’yan Najeriya.
Sultan, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar koli kan Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya fadi haka ne a wani taron gaggawa na Hukumar Zabe da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Kasa ta yi a ranar Talata a Abuja.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa taron na gaggawa ya zama dole ne saboda rikice-rikicen zamantakewar da ke faruwa a wasu sassan kasarnan wanda ya samo asali daga zanga-zangar EndSARS.
Sultan din ya kuma yi kira ga dukkan ‘yan siyasa da su yi aiki don samun kyakkyawar kasa, yana mai cewa“ idan da gaske muna son kasar nan ta ci gaba dole ne mu sauya yadda muke yin abubuwa. ’’
“Sako na ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne, ina kira gare shi da ya kasance mai adalci a ko da yaushe a cikin duk abin da yake yi. Ina kuma bai wa gwamnoni shawarar su kasance masu adalci a koyaushe a cikin duk abin da suke yi.
Adalci yana da mahimmanci a cikin kowace al’umma mai tasowa, al’umma har cikin gidajenmu idan babu adalci ba za’a sami zaman lafiya ba.
“Idan ka ga matsaloli suna faruwa ta ko’ina a ko’ina, akwai matsala game da adalci kuma wannan shi ya sa ba mu da mafita mai kyau.
“Sheikh Usman Danfodio ya ce al’umma za ta iya jurewa tare da kafirai amma ba za ta iya jurewa da rashin adalci ba. Adalci shi ne ginshikin zaman lafiya a kowace al’umma, ’’ in ji shi
Ya ba da tabbacin cewa majalisar sarakunan gargajiya a koyaushe a shirye take ta yi aiki tare da maida kasar nan mafi kyawun inda za a sami zaman lafiya da adalci.
“Kamar yadda na fada koyaushe babu wata cibiya a kasar nan kuma hakika a duniya da za ka iya samun irin mutanen da muke da su a Majalisar Sarakunan Gargajiyar Najeriya.
Mu mutane ne daga kowane fanni, daga mafi kyawun sana’a, sojoji wanda wasunmu ke ciki, zuwa injiniyoyi, zuwa jami’an kwastan da furofesoshi na jami’o’i.
“Za mu kasance masu saukin kai, masu budi da gaskiya a kan dukkan al’amuran kasa kuma za mu aika da shawarwarinmu ga Shugaban kasa don aiwatarwa, ” in ji shi.
Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, Ojaja II, ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta bullo da wasu dabaru da za su kawo kusancin gwamnati ga mutane da nufin taimakawa cibiyoyin gargajiya.