Labarai

Ku kawo karshen tashin farashin kayayyakin Abinci a Nageriya ~Khalifa Sanusi Lamido ya shawarci Babban bankin Nageriya CBN.

Spread the love

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) kuma Sarkin Kano na 14, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya shawarci gwamnan babban bankin Najeriya na CBN, Olayemi Cardoso, kan daukar matakan da suka dace don rage hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya.

Khalifa ya bayyana damuwarsa kan yadda hauhawar farashin kayayyaki tare da daukaka dukiyar daidaikun mutane ya kuma bukaci CBN da ta ci gaba da aiki tukuru wajen ganin an dakile hakan.

Ya kuma jaddada muhimmancin tsare-tsare na dogon lokaci, ya bukaci hukumomin kudi da su mai da hankali kan noma da ilimi, ya kuma yi alkawarin tallafa wa manufofin CBN.

Cardoso ya sake nanata yadda babban bankin CBN ya mayar da hankali kan daidaiton farashi da kuma kudurinsa na yin tasiri ga rayuwar mutane ta hanyar manufofinsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button