Ku Kwantar Da Hankalinku, APC Zata Lashe Zaben Edo A Kotu, Inji Gwamnan Imo.
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya yi watsi da sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar.
Uzodinma ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa daga Babban Sakataren yada labaran sa, Oguwike Nwachuku.
Ya ce dukkan ayyukan da aka yi a jihar Edo sun gamu da matsaloli daga jami’an hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, wadanda suka yi zagon kasa ga tsarin, wanda hakan ya sanya ba za a iya kirga kuri’un APC ba.
Gwamnan ya kara bayyana halayen jami’an INEC a Edo a matsayin ‘abun kunya’.
“Gwamnan ya kuma godewa dan takarar gwamna na APC a Edo, Fasto Osagie Ize-Iyamu, saboda juriya da hakurin da ya nuna.
Ya kuma ba da tabbacin cewa tuni APC ta fara tattara shaidu don shigar da kara a gaban kotun sauraron kararrakin zabe kowane lokaci daga yanzu, yana da yakinin cewa jam’iyyar za ta samu hukunci a kan kari.
“Gwamna Uzodinma ya bukaci dukkan masu biyayya ga APC da magoya bayan jam’iyyar na jihar da su kwantar da hankulansu tare da bin doka, lura da cewa abin da ya faru a jihar Edo zagon kasa ne ga dimokuradiyyarmu mai wahala a Najeriya,” kamar yadda sanarwa ta fada.
A ranar Lahadi ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta bayyana Obaseki a matsayin wanda ya lashe zaben.
Ya sami kuri’u 307,955 a kananan hukumomi 18, inda ya kayar da Ize-Iyamu, wanda ya samu kuri’u 223,619.