Ku Manta Da Batun Sake Bude Boda A Yanzu, Kuci Abinda Muke Nomawa A Gida, Sakon Buhari Ga ‘Yan Najeriya.
Shugaba Muhammadu Buhari a karshen mako, ya ce gwamnatinsa ba ta shirya sake bude kan iyakoki ba a yanzu, yana mai kira ga ’yan Najeriya da su cinye abin da aka samar a cikin gida.
Da yake jawabi ga manema labarai a Filin jirgin saman Sir Ahmadu Bello da ke Birnin kebbi a yayin rangadin don duba irin barnar da ambaliyar ta yi wa Jihar Kebbi kwanan nan, Shugaban, wanda Ministan Noma, Mohammed Sabo Nanono ya wakilta, ya ce Gwamnatin Tarayya Gwamnati a shirye take ta baiwa manoma karfin gwiwa don bunkasa noman gida da kuma fitarwa Kasashen ketare.
Ya bayyana cewa shinkafar da ake nomawa a jihohin Neja, Taraba, Jigawa da Kebbi kadai za ta iya ciyar da kasarnan baki daya, yana mai tambaya: “Don me za mu shigo da abinci alhali za mu iya samar da shi?”
Buhari ya baws mutanen tabbacin goyon baya a noman rani da ma bayansa.
A nashi matsayin, ministan ya ce: “Shugaban kasa ya aiko ni in zo in ga irin barnar da aka yi a Jihar Kebbi. Kuma na gani. Za mu yiwa jihar Kebbi diyya fiye da sauran jihohin. ” Ya gargadi wadanda abin ya shafa da kada su kasance masu yanke kauna, ya kara da cewa gwamnati mai ci za ta dawo da su, ya kara da cewa ma’aikatarsa na hada gwiwa da ma’aikatanta.