Kasuwanci
Ku Nemi Tallafin Biliyan 75 Dana Ware A Baku Dan Sana’a ,Shugaba Buhari Ya Gayawa Matasan Najeriya
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bukaci matasan Najeriya da kada su yi kasa a gwiwa su nemi tallafin kudinnan da ya ware watau Biliyan 75 dan a basu su yi sana’a.
Shugaban ya bayyana hakane a yau a matsayin sakonsa na ranar matasa ta shafinshi na sada zumunta. Hutudole ya kawo muku cewa shugaba Buhari yace kwanannan suka kaddamar da shirin ware Biliyan 75 a matsayin wani yunkuri na samarwa matasa ayyukan yi.
Shugaban yace zai yi amfani da wannan rana ta matasa ya bukaci su nemi wannan tallafi dan damace a garesu.