Labarai

Ku sauke farashin man fetir domin Al’ummarmu na Shan bakar wahala ~Gwamnan Kano Abba Gida-Gida ga Yan kasuwa.

Spread the love

Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusif ya bukaci ‘yan kasuwar man fetur da su saukar da farashin man fetur a kasa domin rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta a halin yanzu.

Gwamnan ya ce yana sane da cewa har yanzu ‘yan kasuwar na da tsohon man da ya kamata a sayar da shi a kan farashin da ya gabata.

Domin rage wahalhalun da ‘yan jihar ke fama da su, ya kamata ‘yan kasuwa su yi hakuri su sake bude duk gidajen mai da kayayyakin da ake da su a hannun jari don sayarwa a kan tsohon farashi.

“A matsayina na Gwamna, na ji takaicin ganin yadda Al’ummarmu na Kano ke shan wahala sakamakon hawan man fetur da bai dace ba, kuma dole ne a kawo karshen lamarin nan take.” Inji Gwamnan.

Kano a cewar Gwamna Abba Kabir, ita ce cibiyar kasuwanci a yankin arewacin kasar da kuma wasu kasashe a yammacin Afirka, kuma al’ummarta masu tarin yawa na ci gaba da samun kyakkyawan yanayin kasuwanci.

Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar Kano nagari da su ci gaba da natsuwa da bin doka da oda domin gwamnati a kodayaushe a shirye take ta tabbatar da cewa mutane suna gudanar da harkokinsu cikin sauki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button