Ku Shirya Nemawa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa Mafaka~Minista Sadiya Ta Fadawa Gwamnoni
Ministar Ma’aikatar Agaji, Cigaban Al’umma da Kare Afkuwar Bala’i, Sadiya Umar Farouq ta ce ƙaramar hukuma 377 na jiha 36 ne aka yi hasashen za su fuskanci ruwan sama mai yawa da ambaliyar ruwa a wannan shekara.
Ministar ta bayyana haka cikin wata yekuwa da ta yi, inda ta shawarci jihohin da suke cikin jerin da su nemi kan tudu domin gina mafaka ga mutanen da ruwan zai raba da mahallansu.
Ambaliyar ruwa ta baya-bayan nan a wasu yankuna ta tabbatar da buƙatar da ake da ita ta ɗaukar matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a wuraren da ake tsammanin ambaliyar, in ji ta.
Hasashen 2020 na ruwan sama da kuma ambaliya ya nuna za a samu ruwa mai yawa a ƙaramar hukuma 102 na jiha 28, yayin da ƙaramar hukuma 275 a jiha 36 – har da Abuja – za su fuskanci matsakaiciyar ambaliyar ruwa.
Sauran ƙaramar hukuma 397 na cikin waɗanda ba sa fuskantar hasashen ambaliya mai girma. Abin baƙin ciki, tuni ambaliyar ta fara faruwa a yankunan jihohin Bauchi da Kebbi da Jigawa. Saboda haka yana da kyau a ɗauki duk matakin da ya dace don kauce wa faruwar hakan.
Daga Amir sufi