Tsaro

Ku yi aiki tare da sarakunan gargajiya don kawo karshen rashin tsaro – Sarkin Awe Umar ya fadawa gwamnati.

Spread the love

Mai martaba Sarkin Awe a jihar Nasarawa, Alh. Isah Abubakar Umar ya gabatar da cewa sarakunan gargajiya na da gagarumar rawar takawa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin kasa.

Sarkin ya bayyana hakan ne yayin ziyarar ta’aziya ga mai martaba Sarkin Kaura Namoda, Maj. Sanusi Muhammad Asha, (rtd) wanda wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kashe mataimakansa takwas a watan Disambar bara.

Don haka, basaraken ya yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su sanya sarakunan gargajiya cikin shirin a matsayin masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, ya kara da cewa ya kamata a ba su cikakken goyon baya don taka rawar da tsarin mulki ya ba su wajen magance matsalar tsaro

Da yake mayar da martani, Sarkin Kaura Namoda, Maj. Sanusi Muhammad Asha, (mai ritaya) ya yaba wa Sarkin na Awe kan ziyarar, yana mai cewa ana shirin hada kai don dawo da matsayin sarakunan gargajiya a harkokin mulki da tsarin gine-ginen kasar.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da cibiyoyin gargajiya da su ci gaba da aiki a matsayin iyakoki wajen magance matsalolin tsaro da samar da hanyoyin ciyar da kasar nan gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button