Siyasa

Kudaina Rokona Akan Maganar Fitowa Takarar Sanata, Zanyi Ritaya A Shekarar 2023 — Kalaman Masari Ga Magoya Bayansa

Spread the love

Daga Miftahu Ahmad Panda

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, Ya Bayyana cewar Bazai Sake Neman Wata Kujerar Siyasa ba Bayan Ya Kammala Wa’adinsa na Biyu a Shekarar 2023,

Wadannan Kalamai na Gwamna Masari dai na Zuwa ne a Matsayin Martani Ga Labaran da Suke ta Zagayawa Akan Cewar Zai Kasance Daya Daga Cikin Masu Neman Kujerar Dan Majalisar Dattijai a Jihar ta Katsina, Bayan Kammala Wa’adinsa na Biyu a Matsayin Gwamnan Jihar ta Katsina,

Wadanne dai Suke Bukatar Masari Yafito Takarar Majalisar Dattijan Suna Kafa Hujjane da Kokari Tareda Ayyukan Cigaba da Yasamar a Lokacin da yake a Matsayin Dan Majalisar Tarayya Dakuma Yanzu da Yake a Matsayin Gwamnan Jihar.

Saidai a Jawabin da Yayiwa Manema Labarai a Jiya Juma’a dake Zama a Matsayin Ranar Demokradiyyar Kasarnan, Gwamnan Jihar ta Katsina ya Bayyana cewar, Bazai Karbi tayin da Magoya Bayansa Suke yimasa ba Kan Batun cewar Yafito Takarar Dan Majalisar Dattijai a Shekara ta 2023,

Haka Zalika Masari Yabayyana cewar a Lokacin da Zai Kammala Wa’adin Mulkinsa na Biyu, Ma’ana a Shekarar 2023 yanada Shekaru 73 a Duniya.

Saboda Haka Me Yake Bukata da Yahuce yaje Yahuta Da Iyalinsa ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button