Kullum Abdullahi Abbas Kara kashe mana APC yake da Bakin jininsa ~Inji Muaz Magaji
Tsohon Kwamishinan Ganduje Muaz Magaji win-win Ya Caccaki tsohon Shugaban Jam’iyar APC Abdullahi Abbas Kan Kalaman sa na Cewa duk wani Wanda Gwamnatin Jihar kano zata dauka Aiki dole sai Ya nuna Katin Zama Dan Jam’iya Lamarin da Muaz Magaji Yace Sam Wannan kalamai Basu dace da Shugaban mulkin Siyasa ba, ga dai Abinda Muaz Magaji ya rubuta a shafinsa na Facebook inda yace Wannan kalamai basu dace da Shugaba ba a tsarin dimocradiyya ballantana ma ace shugaban Jaha guda kamar Kano.
Sam Abdullahi Abbas, bai dace ya zama Shugaba a siyasa ba…kullum yana kara mana kiyayya ne ba soyayya ba……maganar gaskiya itace lokaci yayi da ya kamata a sallame shi ya kama wani aikin can da zai kasaitarsa ba tare da yayi mana barin tafiya ba…
Don mu bama masa kyashi!
Idan har mukai shiru da ire iren wannan katobarar, Kanawa ba za su ce damu komai ba..Amma ta ciki na ciki, sai ranar alkalanchi…2019 darasi ne!.
Rikincin siyasa dai na Cigaba da faruwa tsakanin Abdullahi Abbas da Muaz Magaji…