Labarai

Kullum Siyasar Gidan Malam Shekarau karewa take Kamar kyandir ~Inji Muaz Magaji win-win.

Spread the love

Tsohon Kwamishinan Ganduje Muaz Magaji win-win ya Caccaki Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau bisa hada Kai da Shugaban riko na Jam’iyar APC a jihar Abdullahi Abbas. Tun Farko dai Muaz Magaji ya Fara wallafa hoton Shekarau yama kalubalantarsa kan rikicewar lisaafin rigar da ya saka a Ranar rantsar da Shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar kano.

Yau dai Muaz Magaji ya dauki Tsawon awanni Yana Maganganu a kan Malam Shekarau, ga kadan daga Cikin rubuce rubucensa Kamar Haka…”Yau na san tunanin ‘yan gidan Mallam Shekarau a APC…gaskiya tafiyar gidan akwai matsala! Shi yasa suke ta karewa a siyasar Kano kamar kyandir!”

Welcome on board..
“Yaran Mallam Shekarau sun shigo ajin farko na Dimukradiyya rigar ‘yanchi! Sai dai sun shigo da kafar hagu tare da tsiya tsiya.
Allah ya kyauta bari ba kwashewa, Mallam Ibrahim Shekarau mutumin kirki amma za su kai shi su baro.

Lallai rana office tare da rashin tawakkali sai addua, dama yaran gidan Mallam Sherau irin tarbiyyar su ta siyasa kenan, kiri kiri suna kallon barna amma su dage kan assasata…to meye na jajibo Audu Chiranchi? nifa mamaki ya kamani don na dade rabona da gidan!
Aiko sai dai kuyi tayi..indai jingina da wannan ne tunanin Mallam, to sai dai muce Allah ya kyauta! Muna taya Mallam Jaje!”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button