Rahotanni

Kun sa talakawa sun zabi Buhari yanzu kuma kunyi shiru ana kashesu

Tsohowar jarumar cannywood Rahama hassan tace da yan cannywood

Gareku Yan Kanywood da duk wasu mashhuren Mutanen da suka taya Jam’iyar Apc Tallata Mai Girma Shugaban Kasa na neman takara zango na biyu karkashin Taken NEXT LEVEL

Kunyi amfani da Soyayar da talakawan wannan kasa suke muku kuka saka su suka sake zabe Mai girma shugaba Buhari, kuma sun amsa sun zabe shi.

To in har da Gaske kunyi hakane don Son ganin anyi gyara a wanann kasa ne to yana da kyau ku fito ku sanar da Mai girma Shugaban Kasa Halin da Talaka yake ciki na rashin tsaro da yake fama dashi a wannan kasar.

ku masa kira ta shafukanku da kuka tayasa yakin neman zabensa
Domin wallahi akwai Kauyuka da yawa da basu iya bacci mai kyau da daddare saboda Fargaba da tsoro da yake addabansu,
Idan bakuyi haka ba wallahi ku tabbata kunci Amanan Talakan Nigeria da Masoyan ku.

Allah kawo mana karshen wannan Masifa ya Kawo mana zaman Lafiya da Kwanciyar hankali.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button