Kunce Ni Da Dino Malaye Ne Muke Hana Buhari Aiki, Gashi Yanzu Bama Majalissa Kuma Al’amura Sunfi Da Lalacewa, Inji Bukola Saraki.
Tsohon shugaban majalisar Dattijan Najeriya Abubakar Bukola Saraki ya ce lokacin da yake shugaban majalisar dattijai anyi ta zargin cewa shi da Dino Malaye su suke hana shugaba Buhari gudanar da duk wasu ayyuka na cigaba.
Saraki ya ce amma kuma gashi yanzu ba sa majalisar al’amura kuma sai kara rincabewa suke yi a Najeriya.
Idan baku manta ba a waccan gwamnatin ta shugaba Muhammadu Buhari ‘yan Najeriya sun yi ta magan-ganu akan Bukola Saraki da Dino Malaye, suna cewa wai su suke hana ruwa gudu wajen aiwatar da manyan ayyukan alkhairin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yake son aiwatarwa.
Haka zalika shima shugaban ya sha yin korafin cewa ba ya samun goyon baya daga majalissar Dattijan da Bukola Saraki yake jagoranta a wancan lokacin.
Daga Kabiru Ado Muhd