Kundin tsarin mulkin da ya baka ‘yancin zama gwamnan jihar Ondo shine ya bawa Fulani makiyaya ‘yancin yin rayuwa a duk yankin da suke so, Martanin Buhari ga gwamnan Ondo akan korar Fulani.
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya yiwa gwamnan jihar Ondo gargadi kan korar Fulani makiyaya daga jihar sa.
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ta bakin maitaimaka masa kan harkokin yada Labarai, Malam Garba Shehu ya gargadi gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu da masu goya masa baya kan maganar korar Fulani makiyaya daga jihar sa.
Malam Garba Shehu ya ce Fulani makiyaya su ma ‘yan kasa ne suna da ikon da za su yi rayuwa a duk yankin da suke so.
Malam Garba Shehu ya kara da cewa kundin tsarin mulkin da ya bawa gwamnan jihar Ondo ‘yancin neman takarar zama gwamnan jihar Ondo shine ya bawa Fulani makiyaya ‘yan cin yin rayuwa a duk yankin da suke so.
Garba Shehu ya ce gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu bashi da ikon bawa wasu mutane ko wata kabila umarnin fita daga wani gari ko wani yanki na kasar nan, wannan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa, kuma yunkuri ne na tayar da zaune tsaye wanda ya sabawa dokar kasa.
Daga Kabiru Ado Muhd.