Zamantakewa

Kune Kuke Saka Matsattsun Kaya, Idan Ance ‘Yan Film ‘Yan Iska Ne Hakan Ya Bakanta Muku Rai, Sakon Muhammmad Habibu Abubakar Gombe Ga Nafisa Abdullahi.

Spread the love

Jim kaɗan bayan wallafa hotunanta da jarumar fina-finai kanywood tayi wato nafisa abdullahi a shafinta na facebook mabiyanta keta tofa albarkacin bakinsu akan hotunan, wasu ke koɗata inda wasu kuma ke mata nasiha da taji tsoron Allah.

Hotunan shigar banza ne a fili karara wanda addinin musulunci ya haramta ayi amfani da tufafin da zasu nuna sassa na jiki ‘ya mace.

Kuma har wa yau l’adun mu gabaki ɗaya biyun na hausa fulani basu halastawa ‘ya mace baliga saka kayan da zai fito mata da surar jikinta ba, don haka ba tare da na tsawaita ba nake kira ga wannan jaruma mai suna Nafisa abdullahi da kiji tsoron Allah, ki tuna haɗuwarki da ubangiji a matsayin ku na wandanda kuke ikrarin kawo gyara a alumma.

Kune masu shiga irin wannan idan, ance ‘yan film yan iskane sai abin yabakanta muku rai.

Haba Nafisa kada kici gaba da sanya tufafi irin wannan, domin na yahudawa ne, koyi dasu kuma ba abu bane mai kyau, ki guji haka.

Tarin samin yawan zigi ko yabo alhali kinsan ba akan daidai kike ba, ki kaunace mai gaya miki gaskya akan shigar ki, ko baki shawara don makomar rayuwarki.

Daga karshe ina miki fatan alkhairi Allah shiryar damu daku duka baki ɗaya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button