Kungiyoyi

Kungiyar Arewa Media Writers ta yi Allah wadai da harin ta’addacin da Matasan Yarbawa suka kaiwa Sarkin Fulanin Jihar Oyo, a gaban jami’an tsaron jihar.

Spread the love

…Haka zalika kungiyar ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta daukan mataki kan wannan mummunan harin ta’addacin da aka kaiwa Sarkin Fulanin Jihar.

A jiya Jumma’a da dare matasan Yarbawa da ke jihar Oyo suka kaiwa sarkin fulanin jihar Oyo Alhaji Salihu Abdulkadir, mummunan hari a gidanshi da ke jihar, inda ya samu nasarar ficewa daga gidan tare da iyalanshi zuwa cikin Daji, amma wasu daga ciki sun samu munanan raunuka.

An kaiwa Sarkin Fulanin hari ne a gaban jami’an tsaron jihar, bayan sunsha alwashin za su bashi kariya, amma suka zuba ido suna kallon abin da ke faruwa, ‘yan ta’addan matasan Yarbawan sun samu Nasarar kona gidanshi tare da kona masa motoci Sha Daya, da sauran dukiyarshi da ke gidan baki daya.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar, Alhaji Ibrahim Jiji, ya tabbatar da afkuwar lamarin ga wakilin kungiyar Arewa Media Writers.

“Kamar yadda muka saba fadi, ba dukkan fulani ne bata gari ba. Akwai na gari a cikin mu.

Me za a kira wannan? Wannan mutumin dattijo ne kuma duba yadda aka kai mishi hari tare da koran shi daga gidansa.

Muna bukatar gwamnati ta dauki mataki,” in ji shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar.

Kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani “Arewa Media Writers” ta tana Allah wadai da harin ta’addacin da Matasan Yarbawa suka kaiwa Sarkin Fulanin Jihar Oyo, a gaban jami’an tsaron jihar.

Haka zalika kungiyar tana kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta daukan mataki kan wannan mummunan harin ta’addacin da aka kaiwa Sarkin Fulanin Jihar, matukar ana son a zauna lafiya.

Daga Kungiyar “Arewa Media Writers”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button