Tsaro

Kungiyar Boko Haram ta buɗe gidan rediyo don yaɗa farfaganda.

Spread the love

Kungiyar ISWAP data balle daga Boko Haram ta bude gidan Rediyo dan yada farfaganda ta hanar gizo.

Jaridar HumAngle, ta ruwaito cewa akwai yiyuwar taimakon uwar kungiyar dake kasashen Syria da Iraqi wajan bude wannan gidan rediyon kuma zasu yi amfani dashine wajan neman matsa su shiga kungiyar tasu.

Kafar ta bayyana cewa ta samu kwafin shirye-shiryen gidan rediyon da ISWAP ta yi na ranar 15 ga watan Janairu saidai bata da tabbacin cewa ko an ci gaba da gudanar da gidan Rediyon.

Akwai dai hanya me sauki da ake bude gidan Rediyo ta yanar gizo wadda bata bukatar bude babban guri ko kuma ska manyan injin, wayar hannu da Na’urar Kwamfuta kadai sun isa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button